Fasa gidan yarin na Kogi wani hari ne da wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba da ake kyautata zaton ƴan kungiyar ta’adda ta Boko Haram ne, sun kai hari a gidan yarin Koto-Karffi da ke jihar Kogi a arewa maso tsakiyar Najeriya.[1] Harin ya faru ne a ranar 2 ga watan Nuwamba, 2014.[2] Kimanin fursunoni 144 ne suka tsere daga gidan yarin; An harbe fursuna 1 tare da kashe shi yayin harin.[3] Fursunonin da suka tsere sun kasance suna jiran shari'a ne bisa laifin fashi da makami.[4] Fursunonin 12 sun koma gidan yarin don cika hukuncin da aka yanke musu[5] kuma kusan fursunoni 45 da suka tsere an sake kamo su baki ɗaya.[6][7]